An mika wa majalisa sunayen sababbin Jakadu

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Sanata Saraki ya ce nan gaba kadan za a sanar da sunayen

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika da jerin sunayen sababbin jakadun kasashen waje zuwa ga majalisar dattawa domin tantance su.

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ne ya sanar da haka yayin zaman majalisar a ranar Alhamis.

Kawu Sumaila shi ne mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan majalisar waklilai, ya kuma tabbatar wa BBC batun.

Sanata Saraki ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aike mai kunshe da jerin sunayen.

Sai dai har zuwa yanzu ba a fadi sunayen mutanen ba, amma Saraki ya ce sunayen mutane 47 ne kunshe cikin wasikar.

A yanzu dai Najeriya bata da jakadu a kasashen Biritaniya da Jamus da Amurka da China da Majalisar Dinkin Duniya da Spaniya da Rasha da kuma Faransa, tun bayan da shugaba Buhari ya sauke tsoffin jakadun jim kadan bayan kama aikinsa a watan Mayun 2015.