Abubuwa biyar da ba ku sani ba kan Hillary Clinton

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hillary Clinton za ta zama mace ta farko da za ta yi takarar shugabancin kasa karkashin babbar jam'iyyar Amurka

Hillary Clinton ta samu nasarar zama 'yar takarar shugabancin Amurka, bayan da ta samu goyon bayan adadin wakilan da take bukata.

A yanzu ta zama mace ta farko da za ta yi takarar shugabancin Amurka karkashin babbar jam'iyyar kasar ta Democrat.

Misis Clinton ta rike mukamai da yawa a siyasar Amurka kamar Sanata da kuma Sakatariyar Harkokin Wajen kasar -- amma ko kun san ta taba karbar lambar yabo ta Grammy?

Ga dai wasu abubuwa biyar da baku taba sani ba game da matar tsohon shugaban Amurkar.

Lakaninta shi ne ''Evergreen''

A lokacin da take majalisar dokoki, jami'an hukumar tsaro na kiranta ''Evergreen'', yayin da ake kiran mijinta da suna ''Eagle,'' wato ''Mikiya''.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hillary Clinton ta zama matar shugaban kasa a shekarar 1993

Ta karbi lambar yabo ta Grammy

A shekarar 1997 ne Hillary Clinton ta samu lambar yabo ta Grammy kan kwarewarta wajen iya kalamai kan wasu kalamanta da ka tattara waje daya da ba waka ba.

Kalaman wani littafinta ne mai suna ''It Takes a Village,'' da ta yi kan rainon yara da ilimi, aka nade su a murya. Misis Clinton ta rubuta littattafai da yawa da suka hada da na tarihinta mai suna ''Living History.''

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hillary Clinton ta ci lambar yabo ta Grammy

Ta yi Sanata a lokacin da mijinta ke shugabancin kasa

A shekarar 2000 ne Hillary Clinton ta tsaya takarar majalisar dattawa a jihar New York ta kuma samu nasara, al'amarin da yasa ta zama matar shugaban kasa ta farko da aka zaba a wani mukami. A shekarar 2006 aka sake zabarta da kuri'u masu dumbin yawa.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An zabi Hillary Clinton a matsayin Sanata a shekarar 2000

Ta ki amfani da sunan mijinta

A lokacin da Hillary Rodham ta auri tsohon shugaban Amurka Bill Clinton a watan Oktobar 1975, ba ta yi amfani da sunansa ba.

Duk da haka, makwanni kadan bayan rantsar da Bill Clinton a matsayin shugaban Amurka, sai matar tasa ta sauya sunanta zuwa Hillary Rodham Clinton.

Amma a shekarar da ta gabata ne ofishin kamfe dinta ya sanar da mujallar Washington Post cewa ta fi son a dinga kiranta da Hillary Clinton.

Ba ta iya tuka mota ba

A shekarar 2014 ne a wajen wani taro na kungiyar dilolin abin hawa a New Orleans, Hillary Clinton ta ce rabon da ta tuka mota tun shekarar 1996, kuma babban abin da ke bata kunya a yanzu bai wuce rashin iya tuka mota ba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hillary Clinton ta ce tana jin takaicin cewa a yanzu ba za ta iya tuka mota ba

Ta ce: ''Rabona da tuka mota tun shekarar 1996 kuma ina iya tuna lokacin sosai, kuma abin takaicin shi ne hukumar tsaro ma ta san lokacin, shi ne dalilin da yasa ma ban sake tuka mota ba.''