Kamfanonin jiragen sama na tsaka-mai-wuya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamfanonin jiragen saman kasashen waje sun ce raguwar fasinjoji na daga cikin dalilan da yasa za su bar zuwa Najeriya

Rahotanni na cewa kusan dala biliyan 100 na kamfanonin jiragen saman kasashen waje na iya makalewa a Najeriya.

Wannan na daga cikin dalilan da yasa kamfanonin jiragen sama na Turai guda biyu za su bar zuwa Najeria a yayin da kasar ke cigaba da fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni cikin shekaru da dama.

Kamfanin jirgin saman kasar Spaniya, Iberia, ya soke dukkan jirgensa da ke zuwa kasar a watan da ya gabata, haka kuma jirgin saman Amurka na United Airlines ya ce zai dakatar da harka a Najeriya a karshen watan Yuni.

Kamfanonin jiragen saman sun ce raguwar fasinjoji da takunkunmin da aka saka kan hada-hadar kudaden waje na daga cikin dalilan da yasa suka yanke wannan shawarar.

Wannan dai na daya daga cikin misalai na irin matsalar tattalin arziki da Najeriya ke cigaba da fuskanta.

Faduwar farashin mai a duniya yasa bunkasar tattalin arzikin kasar ya yi kasa, kuma hakan ya jawo raguwar kudaden da kasar ke da su a asusun ajiyarta na kasashen waje.

Hakan kuma ya shafi kamfanonin jiragen sama ta hanyoyi biyu, sun ce kasuwancinsu na fuskantar koma baya.

Sannan suna fuskantar matsala wajen yin sauyin kudin kasar da suke samu zuwa kudaden kasashen waje.

Sai dai wasu kamfanonin kasashen waje kamar British Airways da Emirates za su cigaba da zirga-zirga a Najeriya.