An daure mataimakin shugaban kasar Maldives

Ahmed Adeeb Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon mataimakin shugaban kasa Ahmed Adeeb

Kotu a Maldives ta yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar, Ahmed Adeeb daurin shekara 15 bayan ta kama shi da hannu wajen kitsa makircin halaka shugaban kasar.

An kama Ahmed Adeeb ne da hannu wajen ta da wani bam a cikin wani kwale-kwalen shugaban kasar mai dan karen gudu, a bara.

A farkon wannan makon ne aka yanke wa tsohon mataimakin shugaban kasar wani hukunci na daurin shekara 10, bayan kotu ta kama shi da laifin mallakar wasu makamai.

Ahmed Adeeb dai shi ne jami'in gwamnati mafi girma da aka garkame a gidan yari, tun lokacin da shugaban kasar, Abdulla Yameen ya hau karagar mulki, wato a shekara ta 2013.

A halin da ake ciki dai, baki dayan abokan masu adawa da shugaban kasar daga wadanda suke daure a gidan kaso, sai wadanda suka yi gudun-hijira.

Masu rajin kare hakkin bil'adama dai sun soki shara'ar da ake yi wa 'yan siyasa a Maldives da cewa ba a bin ka'ida.