Ana bankwana da Muhammad Ali

Image caption Muhammad Ali ya kashe maza da yawa.

Ana sa ran dubban mutane ne za su yi wa zakaran damben duniya Muhammad Ali bankwana idan aka yi masa Sallar jana'iza a ranar Juma'a.

Jarumin fina-finai Will Smith da kuma tsohon dan dambe Lennox Lewis na cikin mutanen da za su yi masa bankwana, yayin da tsohon shugaban Amurka Bill Clinton zai jawabin yabo ga shahararren dan damben.

Muhammad Ali ya rasu a makon jiya, yana da shekara 74 a duniya.

Dubban musulmai daga sassa daban-daban na duniya ne suka yi masa addu'o'in a zauren Freedom Hall da ke garin Louisville, wato mahaifar marigayin.

Jama'a kuma sun yi ta yin kabbara a lokacin da aka shigar da gawar Muhammad Ali cikin zauren.

Manyan 'yan damben duniya da masu rajin kare hakkin bil'adama, su ma sun halarci wajen adu'ar.

Babban limamin Carlifornia Malam Zaid Shakir shi ne ya ja sallar jana'izar, kuma yana tare da marigayi Muhammad Ali a lokacin da Allah ya masa cikawa.

A zauren Freedom Hall ne dai marigayin ya yi arangamarsa ta karshe a gida, a sana'arsa dambe.