Sojin Nigeria sun musanta kisan 'yan Biafra

Masu fafutukar Biafra Hakkin mallakar hoto
Image caption Nigeria ta haramta kungiyoyin masu fafutuka na kafa Biafra

Rundunar sojin Nigeria ta yi watsi da rahoton kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International cewa tana da hannu a kisan wasu fararen hula masu goyon bayan kafa Jamhuriyar Biafra.

Amnesty ta ce ta samu rahoton cewa akalla mutum 40 ne aka kashe sannan aka jikkata fiye da 50 a lokacin bikin tunawa da fafutukar kafa Jamhuriyar Biafra a garin Onitsha, a watan jiya.

Kungiyar ta kara da cewa ta samu hujjojin da ke nuna cewa sojojin Nigeria sun bude wuta kan mambobin kungiyar 'Yan Asalin Yankin Biafra (IPOB) da kuma 'yan kallo a wurare uku.

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin ta ce 'ya'yan kungiyar ta Ipob "sun yi zanga-zanga hade da ta-da-zaune-tsaye ba tare da la'akari da doka da oda ba".

Ta kara da cewa jami'an tsaro sun yi aikinsu ne na tabbatar da zaman lafiya.

Tashin hankalin da ya faru shi ne na baya-bayan nan a jerin rigingimun da ake fama da su tsakanin jami'an tsaro da masu fafutukar kafa Jamhuiyar ta Biafra a Kudancin Nigeria.