An fara shari'ar kisa kan 'batanci' ga Annabi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar 28 ga watan Yuni za a cigaba da shari'ar

Yan sanda a Kano, Nigeria, sun gurfanar da wasu mutane biyar a gaban kotu bisa zargin kisan wata mata da suka zarga da yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

A makon da ya gabata ne aka kama ma mutanen, wadanda dukkansu maza ne, bayan kisan matar a wata kasuwa da ke birnin na Kano, a arewacin kasar.

Lamarin da ya auku a ranar 2 ga watan Yuni, ya janwo suka daga al'ummar Musulmai da na Kirista.

Dangin matar sun musunta cewa ta aikata abin da mutanen suka zarge ta da shi.

Mutanen biyar dai sun musanta zargin da ake musu a wata kotun majistiri da ke jihar kuma.

Za a ci gaba da tsare su a hannun hukuma har zuwa ranar 28 ga watan Yuni inda za a ci gaba da sauraron shari'a.