MTN zai biya Najeria tarar Naira 330bn

Shugaban NCC da na MTN Hakkin mallakar hoto NCC
Image caption Shugaban NCC da na MTN ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar

Kamfanin sadarwa na MTN ya amince ya biya Najeriya tarar Naira Biliyan 330.

A watan Oktoban 2015 ne Hukumar Kula da Kafofin Sadarwa (NCC), ta ci MTN tarar fiye da N1.04tn bayan an same shi da laifin kin yanke layukan wayoyin mutane miliyan biyar da ba su yi rijista ba.

Lamarin dai ya kai bangarorin buyi gaban kotu, inda MTN ya nemi a hana Najeriya cin sa wannan tara.

Sai dai an cimma matsaya bayan an kwashe makonnin ana tattaunawar sulhu tsakanin MTN da NCC da kuma gwamnatin Najeriya.

Neman afuwa

Wannan ya sa MTN ya yadda ya biya Naira biliyan 330 a cikin shekaru uku masu zuwa.

Kazalika kamfanin ya amince ya rika yin biyayya ga dokokin Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar NCC Tony Ojobo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: " Na yi imani MTN sun gane kuskurensu... muna sa ran nan gaba kamfanoni za su rinka bin doka".

Ana sa bangaren, MTN ya ce "ya yi nadamar abin da ya faru tare da neman afuwa kan dalilan da suka kai ga cin tarar sa".

Masu sharhi na ganin cewa sansanta lamarin zai taimaka wa MTN ya mayar da hankalinsa kan ci gaba da harkokin kasuwancinsa.