Mutane 20 sun mutu a harin bam a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

Masu fafutika na kasar Syria dake zaune a Burtaniya sun ce mutane akalla 20 aka hallaka a wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake a wajen birnin Damsacus.

Wani faifen bidiyo daga inda abin ya faru ya nuna yadda hayaki daga ababan hawan dake cin wuta ya turnuke sama, kana ga burbushi da suka watsu a kan titina.

Hare-haren sun faru ne a kusa da wurin ibada na Sayyeda Zeinab, wanda mabiya Shi'a a fadin duniya ke girmamawa.

Yankin ya sha fama da kai hare-haren bama-bamai daga mayakan sa kai na mabiya Sunni na kungiyar I-S, wacce ta ce ita ke da alhakin kai hare-haren na baya-bayan nan.