IS ta kashe mutane 12 a garin 'yan Shi'a

Harin bam a Syria
Image caption Yankin Sayyida Zainab ya sha fama da hare-hare a baya

Akalla mutane 12 sun rasa rayukansu a wasu hare-haren kunar bakin wake da aka kai a wata unguwar 'yan Shi'a a birnin Damascus, na kasar Syria.

Kungiyar da ke ikirarin kafa daular Musulunci ta IS ta ce mayakanta uku - biyu sanye da abubuwan fashewa - daya kuma a cikin wata mota makare da bama-bamai ne suka kai harin.

Lamarin ya auk ne a unguwar Sayyida Zeinab wadda ke da nisan kilomita goma daga tsakiyar birnin na Damascus.

Akalla wasu mutanen 55 sun samu raunuka a sakamakon hare-haren.

Yankin Sayyida Zeinab wuri ne da mabiya darikar shi'a ke zaune, kuma yana fuskantar hare-hare akai-akai daga masu ikirarin jihadi.

Kungiyar ta IS ta ce ita ta kai hare-haren bama-bamai biyu a gundumar a farkon shekarar nan inda mutane fiye da 150 suka rasa rayukansu.

Hare-haren ranar na Asabar ya fi shafar mata da kananan yara.