Buhari ya jinjina wa Amodu Shu'aibu

Amodu Shu'aibu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A yammacin ranar Asabar ne ake sa ran jana'izar marigayin

Shugaban Najeria Muhammadu Buhari ya jinjina wa tsohon kocin Super Eagles, Amodu Shu'aibu, wanda ya rasu yana da shekaru 58.

A sakon ta'aziyyar da ya aike a shafinsa na Twitter, Mista Buhari ya ce ya kadu da mutuwar, yana mai adu'ar Allah ya jikansa.

Amodu, wanda ya jagoranci tawagar Super Eagles har sau hudu, ana kyautata zaton ya mutu ne a lokacin da yake barci a daren ranar Juma'a a garin Benin.

Sakataren Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Nigeria (NFF), Dr. Muhammad Sunusi, ya shaida wa BBC cewa marigayin ya koka cewa yana fama da ciwon kirji.

Mutuwar ta Daraktan kwallon kafa na hukumar ta NFF ta zo ne kwanaki kadan bayan rasuwar tsohon koci kuma kyaftin, Stephen Keshi, wanda ya mutu yana da shekaru 54.

Shugaban Hukumar NFF Amaju Pinnick ya ce: "Wannan wani bala'i ne da ya kara samun mu. Har yanzu muna jimamin Keshi, kuma sai ga Amodu ya tafi."

Amodu ya fara jagorantar Najeriya tun yana dan shekara 36 a shekara ta 1994.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amodu Shu'aibu ya jagoranci Super Eagles har sau hudu

Jami'an NFF sun ce an nemi shi da ya maye gurbin Sunday Oliseh a watan Fabrairu amma ya ki saboda rashin koshin lafiya.

Dr Sanusi ya kara da cewa a yammacin ranar Asabar ne za a yi jana'izar marigayin kamar yadda Musulunci ya tanada, a mahaifarsa da ke jihar Edo a Kudu maso Kudancin Najeriya.

Oliseh wanda ya yi aiki a karkashin Amodu a matsayin dan wasa da kuma koci ya ce wannan ba karamin rashi ba ne.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Na tashi da mummunan labari: Amodu Shuaibu ya rasu. Keshi ne ya fara tafiya ga kuma wannan yanzu. Allah ka kawo mana dauki!"

Marigayin ya samarwa Super Eagles gurbin shiga gasar cin kofin duniya a 2002 da 2010, sai dai bai jagoranci tawagar zuwa gasar ba.

A lokacin sa ne Najeriya ta kare a mataki na uku a gasar cin kofin kasashen Afrika a Mali a shekara ta 2002.