Al-Shabab ta kashe ''yan leken asirin Amurka'

Dakarun kungiyar al-Shabab Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar al-Shabab na fada ne da gwamnatin Somalia

Mayakan kungiyar al-Shabab a Somalia sun kashe wasu mutane shida wadanda suke zargi da yiwa Amurka leken asiri.

Daga cikin wadanda suka kashen akwai Mohamed Aden Nur wanda suke zargi da taimaka wa Amurkawa wajen kaiwa tsohon jagoransu hari inda aka kashe shi.

Mayakan dai sun fille masa kai a gaban wani taron jama'a a yankin kudancin kasar ta Somalia.

Amurka ta sha yin amfani da jirage marasa matuka wurin kai hari tare da kashe manyan jami'an kungiyar.

Kazalika 'yan kungiyar ta al-Shabab sun harbe wasu mutane uku a lokaci guda cikinsu harda mutumin da ya taimaka aka kashe wadanda suka kai hari a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Harin wanda da aka kai a rukunin shaguna na Westgate Mall a shekarar 2013, yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Kungiyar ta al-Shabab ta ce tana kokarin kafa daular Musulunci ne a kasar, inda take fafata wa da gwamnatin Somalia mai rauni, wacce ke samun goyon bayan kungiyar Tarayyar Afrika.