An harbe mawakiya Christina Grimmie

Christina Grimmie Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An harbe Christina ne bayan ta kammala wake

An harbe shahararriyar mawakiyar nan 'yar kasar Amurka Christina Grimmie har lahira a birnin Orlando da ke jihar Florida.

An dai kai mata harin ne a lokacin da ta ke sanya hannu a takardar shaidar haduwa ta ita ga masoyanta bayan ta kammala waka a wajen wani taro da akayi.

Mawakiya Christian Grimmie, mai kimanin shekaru 22, ta mutu sakamakon raunin da ta samu bayan harbin da aka yi mata.

'Yan sanda sun ce dan bindigar da ya harbe ta ya kashe kansa a lokacin da dan uwan mawakiyar ya yi kokarin kama shi.

Tuni dai masoyanta suka fara tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta da mahawara irinsu Twitter, inda suke bayyana alhinin su game da mutuwar mawakiyar.