Dubai: An kwace motoci 80 kan tukin ganganci

Hakkin mallakar hoto Dubai Police
Image caption 'Yan sandan sun ce masu tseren za su biya tara mai yawa

'Yan sanda a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, sun kwace fiye da motoci 80 bayan da aka yi tukin ganganci da su.

Motocin dai suna yin tsere ne ba bisa ka'ida ba, inda suke gudun kilomita 300 a sa'a guda.

Shugaban 'yan sanda Khamis al Muzainah, ya ce wasu direbobin sun cire lambar motocinsu da gangan saboda kada a gane su.

Amma 'yan sandan wadanda ke amfani da motoci masu matukar gudu irin su Lamborghini da Porsche da kuma Aston Martin sun cimma masu tseren har suka kamo su.

Wasu rahotanni sun ce tarar da ake karba kan tsere ba bisa ka'ida ba a birnin na Dubai ya kai dala dubu 27.