Eriteria da Ethiopia na fada kan iyaka

Image caption Taswirar kasar Ethiopia

Rohatanni na cewa fada ya barke a kan iyakar da Eriteria da Habasha ke jayayya akai.

Mazauna garin Tserona dake arewaci sun ce, sun ji musayar wuta da manyan bindigogi.

A baya dai Habasha da Eriteria sun gwabza fada tsawon shekaru biyu da rabi, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

A shekara ta 2000 ne aka sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya da ta kawo karshen yakin, amma duk da haka kasashen biyu sun ci gaba da zaman doya da man ja.