MEND ta gargadi Niger Delta Avengers

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun a farkon shekarar nan NDA ke fasa bututan mai da na gas

Kungiyar MEND mai fafutukar nemawa yankin Naija Delta 'yanci, ta nemi kungiyar Niger Delta Avengers, da ta daina kai hare-hare kan bututan mai da na iskar gas a kasar.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, kungiyar ta MEND ta ce gwagwarmayar da ta yi a baya ta hanyar fasa bututai, ba ta yi maganin komai ba.

A saboda haka ne kungiyar ta gargadi 'yan Niger Delta Avengers da su shiga tattaunawar da gwamnatin kasar take son yi da su.

A makon da ya gabata ne dai 'yan kungiyar ta Niger Delta Avengers suka yi watsi da tayin da gwamnatin Najeriya ta yi musu na neman tattaunawa da su.

Sai dai wakilin BBC Abdullahi Kaura Abubakar, wanda ya taba aiki a yankin, ya ce zai yi wuya mayakan na NDA su saurari kungiyar ta MEND.

Fasa bututan man dai ya jefa kasar cikin halin tabarbarewar tattalin arziki da rashin wutar lantarki, ganin cewa sune ke samar da gas din da ake amfani da shi wajen samar da hasken wutar lantarki.

Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce kasar ta yi asarar naira biliyan 51 cikin watanni hudu, tsakanin Janairu da Afrilu, sakamakon irin wadannan hare-haren.

A baya-bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta kira gwamnonin yankin na Naija Delta domin kokarin gano hanyar da za a bi a sasanta da masu tayar da kayar bayan.