Hare-haren NDA sun jawo asarar N51bn

Hakkin mallakar hoto
Image caption Najeriya ta yi asarar biliyoyin naira saboda hare-haren

Nigeria ta yi asarar naira biliyan 51.388 cikin watanni hudu, tsakanin Janairu da Afrilu, sakamakon hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa kan bututan mai a yankin Naija-Delta.

Wannan na kunshe ne cikin wani bayani na wata-wata da kamfanin mai na kasar NNPC, ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Bayanin ya kuma ce kamfanin NNCPC ya kashe naira biliyan 33.994 wajen gyaran bututan mai.

Ya cigaba da cewa an yi asarar naira biliyan 10.335 na danyen man fetur, da kuma asarar dangogin mai na kimanin naira biliyan 7.059 tsakanin watan Janairu zuwa na Afrilu.

Sharhi kan hare-haren Niger Delta Avengers
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan bindigar sun fasa bututan mai da dama

Wannan asara da kasar ke tafkawa dai na faruwa ne sakamakon hare-haren da masu tayar da kayar baya na yankin Naija-Delta mai arzikin mai ke yi.

Kungiyar Niger Delta Avengers NDA, ita ce ta wadda ta bullo a baya-bayan nan take kuma aikata irin wadannan ayyuka.

Ta kai hare-haren kan wasu bututan manyan kamfanonin mai kamar Chevron da Shell da Agip da sauran su, tana mai cewa ta dauki matakin ne saboda "rashin adalcin" da ake yi wa mazauna yankin.

Fasa bututan man dai ya jefa kasar cikin halin tabarbarewar tattalin arziki da rashin wutar lantarki, ganin cewa sune ke samar da gas din da ake amfani da shi wajen samar da hasken wutar lantarki.

A baya-bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta kira gwamnonin yankin na Naija Delta domin kokarin gano hanyar da za a bi a sasanta da masu tayar da kayar bayan.

Sai dai kuma daga baya kungiyar ta sanya a shafinta na Twitter cewa ba za ta karbi tayin gwamnatin ba.