Euro 2016: An gargadi Rasha da Ingila

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan kallo ne suka tayar da hatsaniya a filin wasan

Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, ta gargadi Ingila da Rasha cewa za su iya fuskantar kora daga buga gasar Euro 2016, idan aka sake samun hatsaniya daga magoya bayansu.

A wata sanarwa da ta fitar, UEFA ta nuna takaicinta kan rikicin da aka samu tsakanin magoya bayan kungiyoyin wasa na Ingila da Rasha, a gasar wasan Euro 2016 da aka yi a birnin Marseille na kasar Faransa.

Tun da fari dai UEFA ta tabbatar da cewa ta fara daukar matakin ladabtarwa a kan Rasha bayan da wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Rashan suka fara kai wa magoya bayan Ingila hari a karshen wasan da kungiyoyin suka buga.

UEFA ta yi amanna cewa an nuna wariya a wasan kuma ta yi alkawarin karfafa tsaro a wasannin da za a yi a gaba.

Amma hukumar ba ta kaddamar da wani matakin ladabtarwa kan Ingila ba.

Tuhumar da ake wa Rasha ta hada da hatsaniyar da 'yan kallo suka tayar da nuna wariya da kuma harba tartsatsin wuta.

A ranar Talata ne za a yanke shawara kan takunkuman da za a dauka a wajen taron ladabtarwa.