'Shafin neman aiki na wahalar budewa'

Image caption Yadda shafin yake

A ranar Litinin ne gwamnatin Najeriya ta bude shafin intanet na daukar matasa dubu 500 aikin koyarwa, karkashin wani sabon shiri na rage yawan marasa aikin yi a kasar.

Rahotanni da muka samu daga sassa daban-daban na kasar dai sun ce tuni matasa suka fara rububin zuwa shagunan amfani da intanet, sai dai shafin neman aikin yana wahalar budewa.

Amma gwamnatin ta ce komai na tafiya kamar yadda ya kamata.

Shirin samar da ayyukan yin na cikin alkawuran da Shugaba Muhammadu Buhari ya daukarwa 'yan kasar a lokacin da yake yakin neman zabe.

Image caption Matasa na ta rububin neman gurbin aiki ta shafin

An bai wa gurbin samun aikin koyarwar na mutum dubu 500 suna N-Power Teach, a shafin intanet din.

Sannan akwai gurbin bayar da horo kan fasaha na mutum 25,000 mai suna N-Power Knowledge, da kuma N-Power Build, na bayar da horo kan ayyukan gine-gine da koyon girki da gyaran mota na mutum 75,000.

Wakilinmu na Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya je wani shagon intanet don ganewa idonsa yadda al'amarin ke tafiya:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Amma duk da wannan korafi gwamnatin Najeriya ta ce zuwa yammacin Litinin mutane dubu 400 ne suka yi rijista.

Sai dai yin rijistar ba shi ne mataki na karshe na aikewa da takardun neman aikin ba.

Matasan za su yi aikin koyarwa a makarantun firamare da sakandare da malaman gona da malaman kiwon lafiya da kuma koyarwar yaki da jahilci.

Gurbin samar da aikin na N-Power Teacher Corps initiative zai tallafawa matasa marasa aiki dubu 500 na tsawon shekara biyu.

Matasan za su yi aikin koyarwa a makarantun firamare da sakandare da malaman gona da malaman kiwon lafiya da kuma koyarwar yaki da jahilci.

'Albashi'

Baya ga albashin da za a dinga biyansu duk wata na kimanin naira dubu 23, za kuma a bai wa wadanda suka samu aikin komfutoci domin yin aikinsu yadda ya kamata.

Kazalika, komfutar za ta zama ta su bayan kammaluwar shirin.

A cewar gwamnati, wannan shiri wata dama ce ga matasa 'yan Najeriya da za su bayar da gudunmawarsu ga tattalin arzikin kasar, yayin da a hannu guda kuma za su kara samun wani ilimi.

''Hakan zai kuma warware matsalar rashin isassun malamai a makarantu,'' a cewar gwamantin kasar.

Tun bayan wannan sanarwa da gwamnatin Najeriyar ta yi, dimbin matasan da suka kammala karatunsu ba bu aiki suka shiga neman gurbi a wannan sabon shiri.