Mutane da dama sun kife a kogin Argungu

Image caption Jami'ai na ci gaba da aikin ceto a yankin

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da ake ci gaba da nemo wasu da dama bayan wani kwale-kwale ya kife a wani kogi a garin Argungu da ke Arewacin Najeriya.

Kawo yanzu dai ba a san yawan mutanen da ke cikin kwale-kwalen ba a lokacin da ya kife.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi kuma an tsamo gawarwakin mutane uku.

Masu aikin agaji dai sun ci gaba da neman wasu mutane da ake san ran yiwuwar suna da rai da kuma wasu gawarwakin.

A mafi yawan lokuta ana danganta irin wadannan hadarurruka da yadda mutane ke cika kwale-kwale tare da zuba kaya da yawa.