Babu 'kabilanci' a korar manyan sojin Nigeria

Sojojin Najeria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rundunar ba ta bayyana sunayen wadanda ta sallama ba

Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotanin da ke cewa ta kori wasu manyan jami'anta domin rage yawan sojoji 'yan Kudu da kuma karfafa 'yan Arewa.

Wasu kafafen yada labarai sun zargi rundunar ta kokarin dakile 'yan Kudancin kasar da bayar da fifiko ga yankin Arewa, inda Shugaba Muhamadu Buhari ya fito.

Sai dai wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce "an yi wa sojojin 38 ritayar dole ne kamar yadda tsarin dokar aikin soji ta tanadar, ba wai saboda kabilanci ko addini ba".

Sojojin sun hada da "manjo janar-janar guda tara, birgediya-janar 10, kanar-kanar bakwai, laftanar-kanar 11 da kuma manjo guda daya," a cewar mai magana da yawun rundunar Kanar Sani Usman.

A sanarwar da ta fitar tun farko, rundunar ta ce an sami jami'an ne da laifin shiga harkokin siyasa da kuma hannu a cin hanci da rashawa da ya shifi badakalar sayen makamai.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har yanzu sojojin na fafata wa da kungiyar Boko Haram

A watan Fabrairun da ya gabata, rundunar sojin ta sanar da sunayen manyan jami'anta 12 da ake bincika game da satar kudaden gwamnati.

Jami'an sun hada da tsohon babban hafsan sojin kasar Air Chief Marshal Alex Badeh.

An zargi Mr Badeh ne da wasu manyan jami'an soji da karkatar da kudaden da aka ware da niyyar sayen jiragen yaki, zargin da ya musanta.

Wasu rahotanni sun ce an ware kudaden ne a wani bangare na yakin da kasar ke yi da kungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

A baya sojojin kasar da dama sun sha korafin cewa ba su da isassun kayan aikin da za su tunkarar mayakan kungiyar.