An kashe wani mai rufa idon ruwan sama

Image caption Ba a samu isashen ruwan sama ba a garin Kediba Payam tsawon watanni biyu da suka gabata

Mazauna wani kauye da ke Sudan Ta Kudu, sun kashe wani mutum wanda ake zargin yana wani tsafin da ke iya samar da ruwan sama.

Rahotanni daga gidan radiyon Eye na kasar, sun ce a makon da ya gabata ne aka yi wa Taban Uyev, duka har lahira bayan an zarge shi da yin amfani da tsafi wajen hana ruwan sama a Kediba da ke jihar Amadi sauka.

Ba a samu isasshen ruwan sama ba a garin Kediba Payam tsawon watanni biyu da suka gabata, inda al'ummar ke fuskantar wahala wajen samun amfanin gona.

An samu afkuwar irin wannan lamarin a yankin Torita a watan Agusta a lokacin da matasa suka kashe wani wanda ake zarginsa da haddasa fari.