MDD na so a jinkirta mayar da 'yan hijirar Somalia

Hakkin mallakar hoto

Hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasar Kenya da ta dage wa'adinta na mayar da 'yan gudun hijrar Somalia da ke kasar zuwa gida.

Shugaban hukumar, Filippo Grandi, ya shaida wa 'yan jarida a Nairobi, babban birnin kasar, cewa har yanzu babu zaman lafiya a Somalia, saboda haka bai kamata 'yan gudun hijirar da ke zaune a sansanin Daadab na Kenya su koma garuruwansu ba.

A watan da ya gabata ne dai Kenya ta sanar da cewa za ta rufe sansanin da ke Daadab, al'amarin da ya sa shugabannin Somalia suka yi kashedin cewa matakin ka iya sanya 'yan gudun hijrar su zama 'yan ta'adda.

A cikin watan Nuwamba ne dai kasar Kenya ke son mayar da 'yan gudun hijirar su kimani dubu dari uku da hamsin zuwa kasar Somalia.