Ƙungiyar CAN ta zaɓi sabon shugaba

Hakkin mallakar hoto AP

Ƙungiyar Kiristoci ta Nigeria CAN ta zaɓi Supo Ayokunle a matsayin sabon shugabanta.

Mista Ayokunle, wanda babban limami ne a cocin Baptist Convetion zai karɓi ragamar shugabancin ne daga Ayo Oritsejafor.

An dai gudanar da zaben ne babbar cibiyar Kiristoci dake tsakiyar Abuja.

Supo Ayokunle ya yi nasara akan Joseph Otubu na cocin Motailatu Church Cherubim and Seraphim.

A baya bayan nan ƙungiyar ta CAN ta fuskanci rikicin cikin gida, inda wasu suke zargin ƙungiyar ta kauce hanya ta hanyar cusa kai cikin siyasa.

A lokacin shugaban Ayo Oritsejafor wasu sun zargi CAN da tsunduma cikin harkokin siyasa.

CAN dai ita ce ƙungiyar da ta haɗa dukkan Kiristocin Nigeria.

Amma mabiya cocin katolika sun nesanta kansu daga ƙungiyar a shekara ta 2013.

A shekarar 1976 ne dai aka kafa ƙungiyar CAN inda ta haɗe dukkan Kiristocin Nigeria.