Za mu kawo cigaba a kasashen ECOWAS­-Ellen Sirleaf

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf, ita ce sabuwar shugabar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma, wato ECOWAS ko kuma CEDEAO, kuma ta karbi ragamar mulkin kungiyar ne a taron da ya gudana a Senegal.

Yanzu dai Shugaba Sirleaf ta kasance ta farko a matsayin wata shugaba daga Liberia da za ta jagoranci wannan kungiyar.

Shugabar ta Liberia ta ce dama ta san lokacin kasarta zai zo na samun wannan mukami saboda suna daga cikin wadanda suka kafa kungiyar,dan haka shugabar ta bayyana farin cikinta na samun wannan mukami.

To ko wadanne irin cigaba kungiyar ta ECOWAS za ta samu a lokacin mulkin nata?

Ellen Johnson Sirleaf ta ce zata cigaba ne daga inda wadanda suka gabace ta suka tsaya na abubuwan da kungiyar ta sanya a gaba musamman tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasashen kungiyar dama dukkan ayyukan da za su kawo cigaba a kasashen.