An hana jirgin Musulmi tashi a Malaysia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin Rayani na da jirage biyu, kuma kowanne yana daukar fasinja 180 da matuka 8 da kuma ma'aikata 50

Hukumomi a Malaysia sun dakatar da kamfanin jiragen saman Musulmi na farko a kasar, Rayani Air, daga tashi saboda ya karya dokoki.

Hukumar da ke kula da jiragen sama ta ce za ta soke takardun kamfanin na Rayani Air ne saboda fargabar da take yi a kan yanayin lafiyarsa da kuma yadda ake gudanar da shi.

A watan Disamba ne dai kamfanin ya soma aiki, inda yake bayar da abincin halal, sannan ba ya bari a sha barasa, kana dole ma'aikatansa su sanya tufafin da ba sa nuna tsiraici.

Kamfanin yana da jirage biyu samfurin Boeing 737-400, kuma kowanne yana daukar fasinja 180 da matuka jirgi takwas da kuma ma'aikata 50.