Ra'ayoyin 'yan Najeriya a kan shigo da Shinkafa

A Najeriya, bisa ga dukkan alamu ana samun karuwar kiraye-kirayen a soke matakin da gwamnati ta dauka na hana shigar da shinkafa ta iyakokin kasar.

Kira na baya-bayan nan shi ne wanda mai alfarma sarkin musulmi Alh Sa'ad Abubakar ya yi, inda ya ce, lokaci ya yi da gwamnati za ta janye haramta shigar da shinkafar, sakamakon kuncin da al'uma ke fuskanta ta fuskar abinci.

Kuma ya yi kiran ne lokacin wata ziyarar da shugaban hukumar kwastan ya kaiwa mai alfarmar.

Shin ko yaya wasu a Najeriyar ke kallon kiran da Sarkin Musulmin ya yi ga gwamnati?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti