'Mateen ya daɗe yana zuwa gidan 'yan luwaɗi'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Omar Mateen ya daɗe hana hakon 'yan luwaɗi.

Rahotanni daga Amuka na cewa Omar Mateen, mutumin da ya kashe mutum 50 a gidan rawar da 'yan luwaɗi ke yin sharholiya, ya daɗe yana kai ziyara gidan.

Jaridun ƙasar sun ambato wasu da ke mu'amala da gidan rawar na Pulse da ke Orlando na cewa sau dama suna ganin sa a wajen yana shan wani abu, wasu lokuta kusan sau 12.

Rahotannin na fitowa ne bayan hukumar bincike ta kasar, FBI ta ce Mateen ya yi mata waya gabanin kai harin, inda ya yi mubaya'a ga ƙungiyar IS.

Shugaba Barack Obama ya ce babu wata hujja da suka samu da ta nuna cewa an cusawa Mateen tsattsauran ra'ayi ne daga kasashen waje.

'Ya samu tsaurin ra'ayi a Amurka'

Obama ya bayyana cewa Omar ya kai harin ne sakamakon tsaurin ra'ayin addinin da ya samu a cikin Amurka.

Shugaban na Amurka ya ce zai je jihar Florida ranar Alhamis domin ya jajantawa iyalan mutanen da Omar Mateen ya harbe.

Shi kuwa dan takarar neman shugabancin Amurkar, na jam'iyyar Republican, Donald Trump ya bayyana tsarin shige da ficen Amurka a matsayin mai rauni tun da har aka bar iyalan Omar Mateen suka shiga kasar daga Afghanistan.

Sai dai Hillary Clinton, wadda za ta yi wa jam'iyyar Democrat takarar shugabancin kasar, ta ce za ta kawo sauye-sauye da za su hana mallakar bindiga.