Baturen Birtaniya ya damfari Nijar

Image caption Tun shekarar 2013 James McCormick yake tsare a gidan yari saboda damfara

Wata kotu a Birtaniya ta umarci wani dan kasuwar kasar da ya sayar wa kasashe da dama jabun na'urar gane bam, da ya dawo da kudi da kadarori na kimanin dala miliyan 11.

Jim McCormick ya samu tagomashi sosai a harkar sayar da jabun na'urar gane bam din ga kasashe da dama a duniya da suka hada da jamhuriyar Nijar da Iraki.

A yayin da ake sauraron shari'arsa a kotun Old Bailey da ke London a shekarar 2013, alkalin Richard Hone ya ce damfarar da Mista McCormick ya yi "ba shakka" ta sanya rayuwar mutane da dama a hadari.

Image caption Ya sayar wa Nijar da wasu kasashen jabun na'urar gane bam

A ranar Talata ne alkalin ya yanke hukunci cewa a kwace dukkan kadarorin Mista McCormick da kudadensa da ke Birtaniya da kasashen waje.

Alkalin ya kuma bayar da umarnin cewa a bai wa mutanen da mutumin ya damfara kudaden da aka kwace din a matsayin diyya.

Tun a zaman farko na shari'ar a shekarar 2013 aka yankewa Mista McCormick hukunci daurin shekara 10 a gidan yari, inda a yanzu haka yake can.