Boko Haram ta sace wasu mata a Damboa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun kashe mutum hudu.

Rundunar sojin Najeria ta ce wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sace wasu mata a kauyen Kutuva na karamar hukumar Damboa ta jihar Borno ranar Talata.

Kakakin rundunar sojin kasa, Kanar Sani Usman Kukasheka, ya shaida wa BBC cewa mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kuma kashe mutum hudu a harin da suka kai a kauyen na Kutuva.

Ya kara da cewa dakarunsu sun kaddamar da aikin nemo matan.

Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin ke ci gaba da yin nasarar fatattakar 'yan kungiyar ta Boko Haram.