EU: Idan Biritaniya ta ƙi ji ba ta ƙi gani ba

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Osborne zai yi jawabi dalla-dalla a kan yadda lamarin zai shafi tattalin arzikin Burtaniya.

Ministan kudin Burtaniya, George Osborne ya gargadi al'umar kasar cewa za su fuskanci matsalar tsuke bakin aljihun gwamnati da kuma karuwar haraji idan kasar ta goyi bayan fita daga cikin kungiyar Tarayyar Turai a kuri'ar raba-gardamar da za a kada a makon gobe.

Ana sa ran Mista Osborne zai yi wani jawabi nan gaba kadan, inda zai yi bayani dalla-dalla a kan yadda lamarin zai shafi tattalin arzikin Burtaniya.

A cikin jawabin zai bayyana cewa fita daga kungiyar za ta haddasa durkusheyar tattalin arziki, kuma za a samu gibin kasafin kudin kasar da ya zai kai dala biliyon 40.

Sai dai masu goyon bayan fitar Burtaniya daga kungiyar Tarayyar Turan na zarginsa da cusa wa jama'a tsoro, suna cewa suna da nasu tsarin na kyautata rayuwar kasar, ciki har da jadawalin daidaitawa da kungiyar Tarayyar Turan ta fuskar kasuwanci.