An kori kocin Brazil Dunga

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Dunga ya zama kocin tawagar kwallon kafar kasar daga 2006 zuwa 2010

Kasar Brazil ta sallami kocin kungiyar kwallon kafar ta, Dunga, bayan an fitar da ita daga gasar cin kofin Copa America.

Dunga, wanda shi ne kyafin din da ya jagoranci Brazil ta dauki kofin kwallon kafar duniya na 1994, ya zama kocin tawagar kwalloan kafar kasar ne a karo na biyu a shekarar 2014.

Sai dai kasar Peru ta fitar da Brazil daga gasar Copa America a matakin rukuni a karon farko tun daga 1987 bayan ta doke ta da ci 1-0 a birnin Massachusetts ranar Lahadi.

Dunga, mai shekara 52, ya zama kocin tawagar kwallon kafar kasar daga 2006 zuwa 2010, inda ya sa suka dauki kofin Copa America a shekarar 2007.

Ana sa ran za a nada kocin Corinthians, Tite, domin maye gurbin sa.

Tite, mai shekara 55, ya jagoranci kulob din suka dauki kofin gasar Serie A ta Brazil a 2011 da 2015, da kuma Copa Libertadores da ma kofin kwallon kafar duniya na shekarar 2012.