An gano wasu tarkacen EgyptAir

Hakkin mallakar hoto Egyptian armed forces

Mahukunta a Masar sun ce an gano tarkacen jirgin saman EgyptAir wanda ya yi hadari a tekun Bahar Rum, a watan jiya, yana dauke da mutum 66.

Wata sanarwar da kwamitin da ke gudanar da bincike a kan hadarin ya fitar ya bayyana cewa jirgin ruwan da ke laluben sassan jirgin ya gano tarkacensa da dama a wasu muhimman wurare.

Yanzu dai ayarin masu binciken zai shata taswirar da za ta yi cikakken bayani a kan wuraren da tarkacen jirgin suke.

An dai daina jin duriyar jirgin ne bayan tashinsa daga Paris, ya yi wa Alkahira tsinke.

Ba a dai cire rai cewa bom aka dasa wa jirgin ba, kodayake babu wata kungiyar masu tsaurin ra'ayi da ta dauki alhakin kakkabo jirgin.