Facebook: Ba mu da bangare a raba-gardamar EU

Wasu ma'abota facebook a Burtaniya sun yi kukan cewa dandalin na nuna son-kai dangane da kuri'ar raba-gardamar da ake shirin kada a kasar a makon gobe.

Jon Worth ma'abocin Facebook ne, kuma ya shiga dandalin kuma ya ce an bude shafin muhawara a kan raba-gardamar, amma a cewarsa ba a bayar da zabi ga kowa da kowa don bayyana ra'ayinsa.

Hasali ma, Mr Worth ya ce an ba wa masu ra'ayin ficewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar Turai kadai ne suke da damar bayyana nasu ra'ayin a shafin.

Sai dai kamfanin Facebook a nasa bangaren ya ce ba ya nuna bambanci a cikin al'amarinsa.

Kamfanin ya kara da cewa idan mai sha'awar bayyana ra'ayi yana son yin haka ta dandalin, to ya kamata ya yi amfani da kalmar bida ta "EU" domin samun zabin biyu.

A halin da ake ciki da ake ciki dai kamfanin ya cire shafin saboda sarkakiyar da ke tattare da shi.