'Yan siyasar Kenya sun ba hammata iska

Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Gwamnan Nairobi Evans Kidero ya musanta cewa sanata ya naushe shi

An garzaya da gwamnan birnin Nairobi na Kenya, Evans Kidero, zuwa asibiti bayan da wani sanata ya naushe shi.

Sanata Mike Sonko da Mista Kidero sun kaure da fada ne a lokacin da kwamitin binciken kudi na majalisar dattawan kasar ya titsiye gwamnan kan zargin almubazzaranci da kudaden gwamnati.

Sai dai daga bisani gwamnan ya musanta cewa naushin ya same shi.

Ya shaida wa manema labarai cewa, "Bai same ni ba. Tokare hannunsa na yi.''

Ya kuma musanta cewa an garzaya da shi asibiti - lamarin da mai magana da yawunsa Beryl Okundi ya bayyana tun farko.

A karshe kuma ya musanta zargin kisan kan da Sanata Sonko ya yi masa, yana mai cewa "Abin dariya ne.''