Nigeria ta bayar da kai bori ya hau

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Godwin Emefiele shugaban babban bankin Najeriya ya ce matakin zai fara aiki ranar Litinin

Babban bankin Najeriya CBN, ya sanar da wasu sabbin ka'idoji na hada-hadar kudaden waje a kasar domin karewa da kuma farfado da darajar Naira.

Ka'idojin sun hada da kafa sabuwar kasuwa ta musamman wadda za ta rage bukatar kudaden kasashen waje da matsin lambar da kudin kasar ke fuskanta.

Zai kuma bai wa 'yan kasuwa tabbaci domin su san cewar za su samu kudade na kasashen waje da zarar sun bukata.

Babban bankin zai zabi wasu manyan 'yan kasuwa da zai dinga hulda da su, inda bankin zai zuba dala biliyan 10 ga wannan kasuwa.

Wannan mataki dai zai fara aiki ne a ranar Litinin 20 ga watan Yunin 2016.

A sakamakon hakan CBN zai janye gefe ya zama mai sa ido kan yadda abubuwa ke tafiya domin tabbatar da cewa komai na tafiya daidai.

Sharhi, Naziru Mika'ilu, BBC Abuja

Image caption Naziru Mika'il na sashen Hausa ne ya yi sharhin

Matakin dai yana nufin babban bankin Najeriya yana kokarin ganin darajar Naira ta rage faduwar da take yi.

Wasu masana na ganin gwamnati za ta janye hannu ne kan hada-hadar kudaden kasashen waje kamar yadda ta janye hannunta daga tallafin mai, amma dai babu tabbas har sai an ga abin da zai faru nan gaba.

Kafin yin wannan sanarwa, hannayen jari sun tashi a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta kasar da ke Lagos da sama da kashi uku cikin 100.

Wannan na nuna cewa 'yan kasuwa da masana tattalin arziki sun fara amincewa da matakin da babban bankin ya dauka.

Matakin zai kuma iya janyo hankalin masu saka jari na kasashen waje domin kudinsu zai kara daraja.

Amma sabon matakin hada-hadar na iya kara jawo hauhawar farashi da dama ake fama da shi a kasar. Kuma hakan na iya shafar miliyoyin 'yan Najeriya da suke fama da talauci.

Ana alakanta mummunan tattalin arzikin da kasar ta samu kanta a ciki da faduwar darajar kudin kasar.