An gano gawarwakin mutum 34 a hamadar Nijar

Dubban mutane ne ke yin tafiyar mai cike da hatsari Hakkin mallakar hoto

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Nijar ta ce 'yan ci-rani da ke kokarin ketara hamada 34 sun mutu bayan masu fasakwaurin mutane sun yi watsi da su.

Ministan harkokin cikin gida Bazoum Muhammd ya tabbatarwa BBC aukuwar lamarin.

Wadanda suka mutu sun hada da mata, da maza da kuma yara kanana.

Sanarwar ma'aikatar cikin gida ta Nijar ta ce, wadanda suka mutu sun hada da maza 5, da mata 9, da kuma yara kanana 20.

Mutanen dai sun mutu ne tsakanin ranar 6 zuwa 12 ga wannan watan.

Hukumomin Nijar sun gargadi jama'a su guji yin kasadar kokarin ketara hamada.

Koda bara dai akalla mutane 33 sun mutu a hamadar Sahara yayin da suke kokarin tsallakawa kasar Algeria.

Masu kokarin ketarawa Turai dai suna bi ta Nijar inda, kuma wannan ya zama babban kalubale ga hukumomin kasar.