Ana tuhumar matar Omar Mateen

Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta fara yin tambayoyi ga matar dan bindigar nan, Omar Mateen, wanda ya kai hari kan wani gidan rawar 'yan luwadi a Orlando, inda mutum 49 suka mutu.

Kafafen yada labarai a Amurka sun ce matar dan bindigar, wato Noor, watakila ta san lokacin da ya shirya kai harin, don haka da yiwuwar a tuhume ta da laifin kin fallasa shi.

Gidan Talabijin na NBC ya ba da labarin cewa, tun da farko matar ta yi kokarin hana mijin nata kai harin.

A wani labarin kuma, Shugaba Obama ya yi kakkausar suka ga dan takarar shugabancin Amurka, na jam'iyyar Republican ---Donald Trump, sakamakon furucinsa game da harbe-harben da aka yi a Orlando.

A wani jawabi da ya gabatar a fadar White House, Mista Obama ya ce zancen da Trump ke yi na haramta wa musulmi shiga Amurka babu abin da zai yi face yayata farfagandar masu tsaurin ra'ayi, tare da jefa Amurka cikin hadari.

Shugaba Obama ya kara da cewa, mafi abun kunya a tarihin da Amurka shi ne lokacin da ta gallaza wa 'yan kasarta sakamakon tsoro.

Sai dai Mista Trump, a nasa martanin, ya ce ba shi ya kar zomon ba, rataya aka ba shi, don haka bai dace shugaba Obama ya fusata kamar yadda ya yi ba.

Ya ce yau din nan na kalli shugaba Obama yana cike da haushina fiye da wanda ya yi harbin nan, kuma haka mutane da dama suka ce. Haushin maharbin ya kamata ya ji ba nawa ba!