Beraye za su yi zanga-zanga a Kenya

Hakkin mallakar hoto Eric Nathan Alamy Stock Photo
Image caption Za a yi zanga-zangar ne a makon gobe

Jaridar The Star ta Kenya ta ruwaito cewa masu zanga-zanga na shirin yin amfani da ɓeraye 200 a birnin Nyeri da ke tsakiyar kasar.

Jaridar ta ambato shugaban masu zanga-zangar John Wamagata na cewa "za mu kawo ɓeraye 200, kuma za mu zagaya da su cikin gari ".

Jaridar ta ya kara da cewa za a yi zanga-zangar ne a makon gobe domin yin adawa da shirin majalisar dokokin yanki na kashe kimanin $740,000 domin gina asibitin da su kadai za su rika amfani da shi.

A cikin asibitin za a gina wajen motsa jiki da wanka da tausa , a cewar the Star.