Hankalin matasa ya koma kan social media

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK

Wani rahoto ya nuna cewa galibin mata da matasa sun fi dogaro ne da kafafen sada zumunta na intanet, wadanda aka fi sani da social media wajen samun labaran duniya.

Rahoton ya nuna cewa adadin matasan da ke dogaro da wadannan kafafen yanzu ya zarta adadin masu kallon talabijin don jin labaran duniya.

Cibiyar bincike ta Reuters Institute for the Study of Journalism ce ta gudanar da binciken, kuma a cewar rahoton kashi 28 bisa dari na matasa 'yan shekara 18 zuwa 24 sun bayyana cewa suna dogaro ne da social media wajen samun labarai, sabanin kashi 24 bisa dari, wadanda suka ce suna kallon talabijin wajen samun labaran duniya.

Binciken dai ya nuna cewa yadda ake amfani da wayar salula wajen shiga intanet don samu labaran duniya yana taimakawa wajen dakusar da tsofaffin hanyoyin samun labarai, kamar su Radiyo, da Talabijin da kuma jaridu.