Shekara 40 da zanga-zangar Soweto

Image caption Shekaru arba'in ke nan da kewayowar zanga-zangar da aka fara a Soweto.

A Afirka ta kudu, a ranar Alhamis ne ake bikin shekera 40 da kewayowar zanga-zangar da aka fara a Soweto, inda dubban dalibai bakar-fata suka yi maci don nuna rashin amincewarsu da tsarin koyar da su cikin harshen Afirka'an.

Wannan lokaci dai yana da muhimmancin gaske ga gwagwarmayar da ake ta yaki da babakeren da farar-fata ta yi wajen mulkin kasar, duk kuwa da cewa bakar-fata ce mafi rinjaye.

Kuma daruruwan mutane ne suka mutu a rikicin da ya barke a lokacin zanga-zangar, yayin da gwamnati ta yi yunkurin murkushe masu zanga-zangar, matakin da kasashen duniya suka yi tir da shi.

Wakiliyar BBC ta ce harbe wani Yaro har lahira, mai suna Hecter Peterson da 'yan sanda suka yi ya zama wani babban al'amari a lokacin wannan gwagwamayar.

Har yanzu dai dalibai na ci gaba da yin zanga-zanga a kasar, inda suke cinna wa makarantu wuta don nuna rashin amincewa da wasu sauye-sauye.

A halin da ake ciki dai Afirka ta kudu na tunkarar zaben kananan hukumomi, kuma wannan ne ya sa ake ta yin kiraye-kiraye ga matasa da su yi watsi da tsohuwar fahimta ko dabarun matsin-lamba irin na da.