An dabawa 'yar majalisar Birtaniya wuka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jo Cox 'ya majalisa ce ta jam'iyyar Labour a Birtaniya

'Yan sanda a Birtaniya sun ce an kashe wata 'yar majalisar dokokin kasar sakamakon harin da aka kai mata a mazabarta inda aka daba mata wuka.

Wani mutum mai shekara 52 ne dai ya yi wa 'yar majalisar Jo Cox wannan aika-aika, ya kuma bar ta kwance a kasa cikin jini, yayin da shi ma ya samu kananan raunuka.

Mijinta Brendan Cox ya ce za ta so mutane su hada kai domin yakar kiyayyar da tasa aka kasheta.

Tuni dai aka dakatar da kamfe kan batun kada kuri'ar raba gardamar ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, sakamakon harin.

Shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn ya ce, Birtaniya za ta kasance cikin firgici sakamakon wannan kisan gilla, ya kuma bayyana 'yar majalisar a matsayin abokiyar aiki ta gari.

'Shaidun gani da ido'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana bincike a wajen da aka kashe ta

Wani mai shagon shan shayi Clarke Rothwell, wanda ya shaida lamarin ya ce ya ji wata kara kamar fashewar balam-balam.

''Ko da na duba sai na ga wani mutum a tsaye mai kimanin shekara 50 da 'yan kai sanye da hular tashi-ka-fiye-naci da kuma bindiga irinta da a hannunsa,'' in ji Mista Rothwell.

Ya kara da cewa, ''Sai mutumin ya harbi matar sau biyu, ya kuma durkusa ya sake harbinta a fuska.''

''Sai wani mutum ya yi kokarin cafko wanda ya yi kisan, ya kama shi da kokawa amma sai ya fi karfinsa, kawai sai mutumin ya ciro wuka kamar ta farauta ya fara lumawa matar nan a cikinta sau kusan shida. Sai mutane suka fara ihu suna tarwatsewa daga wajen,'' a cewar Mista Rothwell.

Jo Cox 'yar majalisa ce ta jam'iyyar Labour mai wakiltar mazabun Batley da Spen.