Takaddama kan zaben shugaban CAN a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar Kiristoci reshen jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce bata amince da zaben da aka yi na sababbin shugabannin kungiyar na kasa ba.

Kungiyar ta CAN ta jahar Kaduna ta ce ba a bi ka'idoji ba wajen gudanar da zaben.

Amma daya daga cikin shugabannin kungiyar na kasa ya ce masu korafi a kan zaben ba su da hurumi.

Kungiyar CAN dai na da wasu matsaloli inda a shekara ta 2013 mabiya Cocin Katolika suka janye daga cikinta suna zargin kungiyar da kaucewa manufofinta na ainihi.