Ethiopia ta 'kashe masu zanga-zanga 400'

Image caption Mutane 400 hudu ne suka rasa rayukansu a zanga-zangar nuna kin jini gwamnatin Ethiopia

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW) ta ce dakarun tsaron Ethiopia sun kashe fiye da mutane 400 daga cikin wadanda suka yi zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da aka yi na baya-bayan nan.

A wani cikakken rahota da ta fitar kan zanga-zangar da mutanen yankin Oromo suka yi, HRW ta lissafa sunayen fiye da mutane 300 da ta ce an kashe.

Gwamnati ta amince cewa wasu masu zanga-zanga sun mutu sai dai ta ce HRW ta "zake wurin bayyana adadin".

Masu zanga-zangar na tsoron cewa shirin gwamnati na fadada babban birnin kasar zai sa manoma da dama su rasa gonakinsu.

A watan Nuwamban bara ne aka fara boren, sai dai gwamnati ta yi watsi da shirin na fadada Addis Ababa a watan Janairu.

Yankin Oromo shi ne mafi girma a Ethiopia, kuma yana kewaye da birnin.

Sai dai sauya manufar bai hana ci gaba da zanga-zangar ba, amma dai ta ragu.