'Yan gudun hijirar Niger sun galabaita

Image caption Yan gudun hijira a Nijar na cikin mawuyacin hali a inda aka tsugunar da su.

Ministan harkokin cikin gidan Jamhuriyar Nijar, Bazoum Mohammed, ya ce dubban masu gudun-hijirar da rikicin Boko Haram ya tilasta wa barin gidajensu a kasar sun galabaita a sansanonin da aka tsugunar da su.

Kimanin mutum 50, 000 rikicin ya daidaita a Bosso lokacin da mayakan Boko-Haram suka kai hari garin.

Ministan dai ya kai ziyara ne sansanin masu gudun-hijirar, inda ya ce har yanzu jama'a na ci gaba da kwarara, kuma wadanda suka isa sansanin na baya-bayan nan ba sa samun abinci.

Ya bayyana harkokin kiwon lafiya a sansanin da cewar sun tabarbare.

Hukumar samar da abinci ta duniya dai ta ce tana shirin ninka agajin abincin da take kaiwa yankin.