An kai harin kunar bakin-wake Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harin ya kashe mutane 10 kuma ya jikkata wasu 15

Wani harin kunar bakin-wake da aka kai a wajen ofishin 'yan sanda da ke garin Abughrain na kasar Libya ya yi sanadin mutuwar mutum 10.

Wani mai magana da yawun mayakan sa kai, Mohamed El Gasri, ya ce kusan mutum 15 sun jikkata a harin kunar bakin-waken.

Abughrain dai wani karamin gari ne mai nisan kilomita 60 a gabashin Libya kuma shi ne gari mafi girma na uku na yankin Misrata.

A makon jiya ne dai masu yaki da IS, wadanda suka hada gwiwa da gwamnatin Libyar da ke da goyon bayan majalisar dinkin duniya a Tripoli, suka ce sun kwace ikon gabar tekun Sirte daga mayakan IS.

Sirte dai shi ne babban gari da ke karkashin ikon IS baya ga Iraq da Syria.