Wata ta watsa wa saurayinta guba a Pakistan

Image caption Ana yawan samun hare-haren guba duk shekara a Pakistan

An kama wata a Pakistan bayan da aka zarge ta da watsa wa wani mutun guba saboda ya ki yarda ya aure ta.

Mutumin wanda ya haura shekaru 20, ana yi masa magani a asibiti a birnin Multan bayan kusan rabin jikinsa ya kone.

Dangin mutumin sun ce yana soyayya da matar ne sai dai ba ya so ya aure ta.

Sai dai matar ta ce ta kare kanta ne bayan da aka kai mata hari.

Ana yawan samun hare-haren guba a Pakistan duk shekara sai dai ba kasafai ake kai wa maza harin ba.

Lamarin dai ya faru ne a Multan da sanyin safiyar ranar Talata.

'Yan jaridu a yankin sun ce an ga mutumin yana fitowa daga gidan matar yana kuka da guba a jikinsa.

Matar ta kwara wa mutumim gubar ne bayan ya "ziyarce ta sannan ya kara maimaita mata cewa ba zai aure ta".

Mutumin ya juya mata baya, abin da ya sa gubar bata samu fuskarsa ba.