An daure mutanen da suka ƙona Musulmai a India

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen duniya sun yi tur da kisan gillar da aka yi wa Musulmin

Wata kotu a kasar India ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai kan mutum 11 saboda rawar da suka taka wajen yi wa Musulmi kisan gilla a jihar Gujarat a shekarar 2002.

Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekara bakwai ga mutum 12, yayin da mutum daya zai sha daurin shekara 10.

Mutanen sun kai hari lokacin tarzomar da aka yi a Gujarat inda suka kashe Musulmi 69 ta hanyar makurewa sannan suka cinna musu wuta.

Fiye da mutum 1,000 ne suka mutu, akasarin su Musulmi, lokacin tarzomar wacce aka yi sakamakon wutar da ta kama a cikin wani jirgin kasa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar Mahajjata 'yan Hindu 60.