Yunkurin ɗinke ɓarakar shugabancin PDP

Image caption Bangarorin biyu sun amince su gabatar da wakilai hurhudu a tattaunawar sulhun.

A Najeriya, a wani yunkuri na shawo kan rikicin babbar jam'iyyar hamayyar kasar, PDP, Babban Baturen 'yan sandan kasar, Solomon Arase, ya gana da bangaren Sanata Ali Modu Sheriff da kuma Sanata Ahmed Makarfi a ofishinsa da ke Abuja.

A taron da suka yi a ranar Jumma'a, bangarorin biyu sun amince kowannensu ya gabatar da wakilai hurhudu a tattaunawar neman sulhu da za su yi nan da mako guda.

Sai dai Mista Arase ya ce ofishin jamiyyar ta PDP da ke Wadata Plaza da kuma Legacy House za su ci gaba da kasancewa a rufe, har bayan bangarorin biyu sun cimma matsaya.

Jam'iyyar dai na fama da rikicin shugabanci ne bayan wani taro da ta yi ya nada Sanata Ahmad Makarfi a matsayin shugabanta, kana ya sauke Sanata Ali Sheriff, wanda ke shugabancin rikon-kwarya.

Hakan ya fusata Sanata Ali Modu Sheriff, wanda ya garzaya kotu, kuma ta ba shi izinin ci gaba da shugabancin jam'iyyar.

Sharhi - Nasidi Adamu Yahaya, Abuja

Da alama rikicin da ya mamaye jam'iyyar ta PDP ba shi da ranar karewa duk kuwa da yunkurin da rundunar 'yan sandan ke yi na shawo kansa.

Shi dai Sanata Ali Modu Sheriff ya yi ikirarin cewa jiga-jigan jam'iyyar PDP sun amince ya ci gaba da shugabanci zuwa shekarar 2018 a lokacin da aka yi yarjejeniyar ba shi shugabancinta.

Sai dai abin da aka bayyane mutane shi ne, zai kammala shugabancin rikon-kwarya ne a watan Mayun da ya wuce.

Wasu 'yan jam'iyyar dai na ganin jam'iyyar APC mai mulki na da hannu a rikicin PDP, ko da ya ke APC ta musanta wannan zargi.

PDP dai ta yi kaurin-suna wajen rikicin cikin-gida, kuma sau da dama hakan kan kai ga fitar manyan jami'anta.