Ra'ayi Riga: Tsadar shinkafa a Najeriya

A Najeriya, jama'a a kasar na fuskantar matsin rayuwa, sakamakon tashin farashin kayayyakin masarufi, da suka hada da shinkafa. Hakanne yasa wasu shugabannin al'umma a kasar, ciki har da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, bayar da shawarar dage takunkumin shigowa da shinkafa cikin kasar ta iyakokin kan kasa. Shin menene ra'ayin jama'a akan wannan? Maudu'in da aka tattauna akai kenan a filinmu na Ra'ayi Riga.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti